Liverpool da United sun hana magoya bayansu yin rigima

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hukumar kwallon kafa ta Turai ta hukunta kungiyoyin biyu a watan Maris, bayan da ta samesu da laifin tayar da hayaniya a lokacin da suka buga gasar Europa

Liverpool da Manchester United sun bukaci magoya bayansu da su kwantar da hankalinsu a lokacin da za su kara a wasan Premier a ranar Litinin a Anfield.

A cikin watan Maris hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa, ta hukunta kungiyoyin biyu saboda samunsu da laifin tayar da yamutsi a gasar cin kofin zakarun Turai ta Europa.

Kungiyoyin biyu sun fitar da sanarwa ta hadin gwiwa cewar za su gurfanar da duk wanda aka kama da laifin tayar da hayaniya a lokacin wasan.

Karawar da kungiyoyin za su yi a daren Litinin ita ce ta 197 da za su fafata a tsakaninsu.