Ya kamata a bai wa Southgate horar da Ingila — Wenger

England

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Southgate ya yi wa tawagar kwallon kafa ta Ingila wasanni 57

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce ya kamata a bai wa Gareth Southgate aikin horar da tawagar Ingila na tsawon lokaci.

Southgate ya maye gurbin Sam Allardyce a matsayin kociyan rikon kwarya a watan Satumba, bayan da suka raba gari da hukumar kwallon kafa ta Ingila .

Kociyan ya kuma jagoranci tawagar Ingila, inda ta ci Malta 2-0 da kuma yin canjaras da Slovenia a wasan shiga gasar cin kofin duniya.

Wenger ya ce Southgate yana da kwarewar horar da 'yan wasan tamaula, ya kuma san yadda ake jan ragamar tawagar kwallon kafa.

Wenger wanda yarjejeniyarsa da Arsenal za ta kare a karshen kakar bana, an yi ta rade-radin cewar shi ne za a bai wa aikin horar da Ingila.

Southgate mai shekara 46, zai ja ragamar Ingila a fafatawar da za ta yi da Scotland a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya ranar 11 ga watan Nuwamba a Wembley da wasan sada zumunta da Spaniya kwanaki hudu tsakani.