Mascherano zai tsawaita zamansa a Barcelona

Spain

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mascherano zai ci gaba da buga leda a Barca zuwa 2019

Mai tsaron baya na Barcelona, Javier Mascherano, zai tsawaita yarjejeniyarsa ci gaba da taka-leda a Barcelona a ranar Litinin.

Mascherano dan wasan tawagar kwallon kafa ta Argentina zai saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da murza leda a Barcelona zuwa shekarar 2019.

Dan kwallon ya buga wa Barcelona wasanni 289, tun lokacin da ya koma can da taka-leda daga Liverpool a shekarar 2010.

Mascherano wanda yake shekara ta bakwai a Barca, ya lashe kofuna 17 a kungiyar.