Hull City ta nada Phelan a matsayin kociyanta

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Phelan ne ya lashe kyautar kociyan da yafi yin fice a gasar Premier a watan Agusta

Kungiyar Hull City mai buga gasar Premier, ta nada Mike Phelan a matsayin wanda zai ja ragamarta a fagen tamaula.

Phelan ya karbi aikin horar da Hull City a matsayin rikon kwarya, bayan da Steve Bruce ya bar kungiyar.

Kociyan mai shekara 54, ya fara jan ragamar Hull da kafar dama, bayan da ya lashe kyautar mai horar wa da yafi yin fice a gasar Premier a watan Agusta.

Hull, wadda ta doke Leicester da kuma Swansea a gasar Premier bana, za ta ziyarci Bournemouth a ranar Asabar.