Guardiola zai sauya alkiblar kwallon Ingila

England

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Xavi ya ci kofuna biyu na gasar Zakarun Tuari karkashin Guardiola

Tsohon dan wasan Barcelona, Xavi, ya ce yana da amannar cewar Pep Guardiola zai sauya alkiblar kwallon Ingila a lokacin da zai yi yana horar da Manchester City.

Xavi, mai shekara 36, wanda ke murza leda a Al Sadd SC, ya lashe manyan kofuna 14 karkashin Pep Guardiola a shekara hudu da ya yi kocin Barcelona.

Dan kwallon ya ce Guardiola ne kadai zai sauya alkiblar yadda ake murza-leda a Ingila.

Guardiola wanda ya koma horar da Manchester City a kakar bana, ya yi rashin nasara a karon farko a hannun Tottenham, bayan da ya jagoranci City lashe wasanni 10 a dukkan karawar da ta yi.