Arsenal ta doke Swansea City da ci 3-2

Premier

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Sau biyar Walcott ya ci kwallo a wasanni takwas da ya buga wa Arsenal a gasar cin kofin Premier

Arsenal ta samu maki uku a kan Swansea City, bayan da ta doke ta da ci 3-2 a wasan Premier da suka kara a ranar Asabar a Emirates.

Arsenal ta ci kwallayenta ne ta hannun Theo Walcott wanda ya ci biyu a karawar sai Mesut Ozil da ya ci daya.

Swansea wadda sabon koci Bob Bradley ya fara jagoranta ta ci kwallayenta biyu ta hannun Gylfi Sigurdsson da kuma González Tomás.

Arsenal ta karasa wasan da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Granit Xhaka jan kati saura minti 20 a tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon Arsenal wadda ta buga wasanni takwas ta koma mataki na biyu a kan teburin Premier da maki 19.

Ga sakamakon wasannin mako na takwas da aka buga a ranar Asabar:

  • Chelsea 3 Leicester 0
  • Arsenal 3 Swansea2
  • Bournemouth 6 Hull City1
  • Man City 1 Everton 1
  • Stoke 2 Sunderland 0
  • West Brom 1 Tottenham 1