City ta barar da fenariti biyu a karawa da Everton

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sau bakwai golan Everton Stekelenburg ya tare fenariti a karawa da Manchester City

Manchester City da Everton sun tashi wasa kunnen doki 1-1 a gasar cin kofin Premier wasan mako na takwas da suka fafata a Ettihad a ranar Asabar.

Romelu Lukaku ne ya fara ci wa Everton kwallo bayan da aka dawo daga hutu, daga baya ne City ta farke ta hannun Nolito.

City ta barar da bugun daga kai sai mai tsaron raga da Kevin De Bruyne da Sergio Aguero suka buga, inda mai tsaron ragar Eveton, Maarten Stekelenburg, ya hana su shiga raga.

City wadda ta buga wasanni takwas a gasar ta Premier ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburin gasar da maki 19, iri daya da wanda Arsenal keda shi.