Real Betis ta sha kashi a hannun Real Madrid

Spain

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Real Madrid ta koma mataki na biyu a kan teburi da maki 18 iri daya da Atletico wadda ke matsayi na daya

Real Betis ta yi rashin nasara a gida a hannun Real Madrid, bayan da aka sharara mata kwallaye 6-1 a gasar La Liga wasan mako na takwas da suka fafata a ranar Asabar.

Madrid ta ci kwallaye hadu tun kafin a je hutu ta hannun Varane da Benzema da Marcelo da kuma Isco.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Madrid ta kara cin kwallo na biyar ta hannun Isco kuma ta biyu da ya ci a wasan, sannan Cristiano Ronaldo ya ci na shida.

Real Betis ta zare kwallo daya ta hannun Alvaro Cejudo saura minti 13 a tashi daga wasan.

Madrid ta hada maki 18 a wasanni takwas da ta yi a gasar La Liga tana kuma mataki na biyu a kan teburi da maki iri daya da Atletico wadda ke matsayi na daya, bayan da ta casa Granada da ci 7-1 a ranar ta Asabar.