Tennis: Murray ya lashe kofi na shida a bana

Tennis

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Murray ya lashe kofin Shanghai a shekarar 2010 da 2011 da kuma 2016

Andy Murray ya lashe kofin kwararru na Shanghai, bayan da ya doke Roberto Bautista Agut a wasan karshe.

Murray wanda ke matsayi na biyu a iya kwallon tennis a duniya ya yi nasara ne a kan Bautista Agut wanda ke mataki na 19 a iya wasan da ci 7-6 (7-1) 6-1.

Bautista Agut ya kai wasan karshe ne bayan da ya cinye Novak Djokovis wanda ke mataki na daya a duniya a wasan daf da na karshe.

Murray ya lashe kofin kwararru na Shanghai karo na uku kenan, kuma kofi na shida da ya ci a bana.

Murray, mai shekara 29, ya rage saura maki 915 tsakaninsa da Novak Djokovic wadda ke mataki na daya a iya kwallon tennis a duniya.