Alkalin wasa Taylor zai shiga matsi — Mourinho

Premier

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Taylor ya raba katin gargadi a wasa sau 23, har yanzu bai bayar da jan kati ba

Jose Mourinho ya ce alkalin wasa Anthony Taylor zai busa wasan da za a yi tsakanin Manchester United da Liverpool na gasar Premier da gumin goshi a ranar Litinin.

Mourinho ya ce wasu da gangan na kokarin saka matsi a kan alkalin wasan, wanda ke mara wa kungiyar Altrincham baya.

A ranar Litinin tsohon mai kula da harkar wasan tamaula, Keith Hackett, ya soki nada Taylor a matsayin alkalin wasa, saboda yana zauna mil shida tsakaninsa da Old Trafford.

Su ma magoya bayan Liverpool sun yi korafi a shafukan sada zumunta kan nada Taylor a matsayin wanda zai alkalanci fafatawar.

Mourinho ya ce Taylor, mai shekara 53, kwararre ne a kan aikinsa, amma zai yi masa wahala ya jagoranci karawar kamar yadda ta dace.