Nura da Garkuwan Shagon Alabo sun dambata

Dambe
Bayanan hoto,

Turmi uku suka yi babu kisa tsakanin Nuran Dogon Sani da Garkuwan Shagon Alabo

Nuran Dogon Sani da Garkuwan Shagon Alabo sun dambata babu kisa a fafatawar da suka yi a ranar Lahadi a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Nura dan damben Arewa da Garkuwan Shagon Alabo daga Kudu sai da suka yi turmi uku babu wanda ya dafa kasa, alkalin wasa Tirabula ya raba su.

A ranar ta Lahadi da safe, an fara ne da wasa tsakanin Garkuwan Matawallen Kwarkwada daga Kudu da Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa, kuma turmi biyu suka yi babu kisa.

Shi kuwa Dan Kanawa daga Kudu buge Shagon Bahagon Mori daga Arewa ya yi a turmin farko, dambatawa tsakanin Dan Ali daga Kudu da Shagon Sunusi Dan Auta daga Arewa canjaras suka yi.

Sa zare da aka yi tsakanin caka-caka daga Arewa da Garkuwan Autan Faya daga Kudu babu kisa, haka ma wasan Bahagon Sisco daga Kudu da Durago daga Arewa babu wanda ya yi nasara.

Shi kuwa Dogon Minista daga Kudu nasara ya samu a kan Bahagon Abban Na Bacirawa, yayin da aka tashi wasa babu kisa tsakanin Dan Aminu Langa-Langa daga Arewa da Shagon Mada daga Kudu.