Klopp zai karbi bakuncin Mourinho a gasar Premier

Asalin hoton, Getty Images
Wannan ne karo na shida da za a fafata tsakanin Klopp da Mourinho
A ranar Litinin kociyan Liverpool, Jurgen Klopp, zai karbi bakuncin Jose Mourinho na Manchester United a gasar cin kofin Premier wasan mako na takwas a Anfield.
Klopp tsohon kociyan Borrusia Dortmund wanda ke jan ragamar Liverpool ya fafata da Mourinho a lokacin da ya yi kocin Real Madrid da Chelsea.
Cikin wasannin da suka kara a tsakaninsu, Klopp ya ci guda uku, Mourinho ya lashe daya suka yi canjaras a karawa daya.
A yawan cin kwallaye kuwa Mourinho ya ci guda 11, shi kuwa Klopp guda bakwai ya ci a fafatawa biyar da suka hadun.
Ga jerin karawa da suka yi tsakanin Klopp da Mourinho:
- Borussia Dortmund 2-1 Real Madrid (Gasar cin Kofin Zakarun Turai, Oktoba 2012)
- Real Madrid 2-2 Borussia Dortmund (Gasar cin Kofin Zakarun Turai, Nuwamba 2012)
- Borussia Dortmund 4-1 Real Madrid (Gasar cin Kofin Zakarun Turai, Afirilu 2013)
- Real Madrid 2-0 Borussia Dortmund (Gasar cin Kofin Zakarun Turai, Afirilu 2013)
- Chelsea 1-3 Liverpool (Gasar cin Kofin Premier League, Oktoba 2015)