Tennis: Serena na yin jinyar rauni a kafada

Tennis

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Serena ta lashe manyan kofuna 22 a wasan kwallon tennis

Serena Williams ba za ta buga gasar kwallon tennis da za a yi a Singapore a makon gobe ba, Sakamakon jinyar raunin da take yi a kafada.

Rabon da Serena wadda ke mataki na biyu a jerin wadan da suke kan gaba a iya kwallon tennis a duniya tun watan Satumba, a gasar US Open, a inda ta kai wasan daf da karshe.

Watakila Johanna Konta, wadda ke matsayi na tara a kwallon tennis a duniya ta maye gurbin Serena, sai dai ita kuma tana fama da ciwon ciki.

'Yan wasa daga matsayi na daya zuwa takwas da ke jerin wadan da suka fi iya tennis ne ke shiga babbar gasar karshen shekara da za a fafata tsakanin 23 zuwa 30 ga watan Oktoba.

Konta wadda ta kai wasan karshe a gasar da aka yi a China, sai hakura ta yi da gumurzun da aka yi a Hong Kong kuma ba za ta shiga wasannin da za a yi a Kremlin a makonnan.