Drogba ya ki buga wasa saboda yana benci

Asalin hoton, Getty Images
Drogba tsohon dan wasan Chelsea wanda ya bar Stamford Bridge a 2015
Didier Drogba ya ki ya buga wa kungiyar Montreal Impact wasa, bayan da aka fada masa cewar zai fara zaman benci a karawa da suka yi da Toronto, in ji koci Mauro Biello.
Drogba mai shekara 38, bai halarci filin wasa na Sputo a fafatawar da kungiyarsa Impact ta tashi 2-2 da Toronto a wasan cike gurbi a gasar cin kofin Amurka ba.
Tun farko Montreal ta ce dalilin da ya sa Drogba bai buga wasan ba, shi ne jinyar ciwon baya da yake fama da shi.
Ba a fara wasanni biyu da Drogba ba, a cikin karawa hudu da Impact ta yi a gasar ta cin kofin Amurka.
Dan wasan dan kasar Ivory Coast ya ci wa Montreal kwallaye 10 a wasanni 21 da ya yi mata wasanni a bana.