Real ta fitar da 'yan wasan da za su kara da Legia

Asalin hoton, Getty Images
Real tana mataki na biyu a kan teburi a rukuni na shida da maki hudu
Real Madrid ta fitar da sunayen 'yan wasa 19 da za su buga mata wasan da za ta yi da Legia Warsaw a ranar Talata a Santiago Bernabeu a Gasar cin Kofin Zakarun Turai.
Kungiyoyin biyu za su kara a wasa na uku na rukuni na shida, inda Real Madrid ce ta biyu a kan teburi da maki hudu, ita kuwa Warsaw ba ta da maki ko daya.
Wannan kuma shi ne karon farko da Real Madrid za ta kara da kungiyar Legia Warsaw.
Ita kuwa Sporting Lisborn wadda ke mataki na uku a kan teburi za ta karbi bakuncin Borussia Dortmund wadda ke ta daya a rukunin na shida a ranar ta Talata.
Ga 'yan wasan da za suyi wa Madrid wasa:
Masu tsaron raga: Keylor Navas, Casilla da Rubén Yáñez.
Masu tsaron baya: Carvajal, Pepe, Varane, Nacho, Marcelo da Danilo.
Masu buga tsakiya: Kroos, James, Kovacic, Asensio da Isco.
Masu cin kwallaye: Cristiano Ronaldo, Benzema, Bale, Lucas Vázquez da Morata.