Za mu koma kan ganiyarmu — Raneiri

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Leicester City mai rike da kofin Premier tana mataki na 13 a kan teburin gasar bana

Kociyan Leicester City, Claudio Raneiri, ya kare kungiyar saboda kasa cin kwallaye a gasar Premier bana.

Raneiri ya ce za su dawo kan ganiyarsu, kuma haka wasa ya gada wata rana ka taka leda mai kayatarwa wani lokaci ka kasa taka rawar gani.

Leicester wadda ke rike da kofin Premier tana da maki takwas daga wasanni takwas da ta yi, inda aka doke ta a karawa hudu a bana, duk da cewa a bara sau uku aka cinye ta.

Kungiyar za ta karbi bakuncin FC Copenhagen a Gasar cin Kofin Zakarun Turai a wasa na uku a rukuni na bakwai a ranar Talata, tuni kungiyar ta lashe wasanni biyu da yi a gasar.

Leicester City tana mataki na 13 a kan teburin Premier da maki takwas, za kuma ta karbi bakuncin Crystal Palace a wasan mako na tara a ranar 22 ga watan Oktoba.