Liverpool da Man United sun tashi canjaras 0-0

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Liverpool da Manchester United sun raba maki dai-dai a tsakaninsu

An tashi wasa canjaras babu ci tsakanin Liverpool da Manchester United a gasar Premier wasan mako na takwas da suka kara a Anfield a ranar Litinin.

Liverpool ta taka wasa kashi 65 cikin dari, yayin da United ta buga kashi 35, kuma sau 14 Liverpool ta yi laifi, bayan da United ta yi laifi sau 20.

Da wannan sakamakon Liverpool ta hada maki 17 tana mataki na hudu a kan teburi, yayin da United ke matsayi na bakwai da maki 14.

Liverpool za ta karbi bakuncin West Brom a wasan mako na tara a ranar 22 ga watan Oktoba, ita kuwa United za ta ziyarci Chelsea a ranar 23 ga watan na Oktoba.