An amince 'yan kallo 50,000 su kalli wasan Masar

World Cup Qualifier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masar za ta karbi bakuncin Ghana a ranar 23 ga watan Nuwamba

Hukumar kwallon kafa ta Masar ta sanar da cewar za ta bar 'yan kallon kwallon kafa su 50,000 su kalli karawa da kasar za ta yi da Ghana a birnin Alexandria.

Kasashen biyu za su buga wasan shiga gasar cin kofin duniya a ranar 13 ga watan Nuwamba a filin wasa na Borg El Arab.

Hukumar kwallon kafa ta Masar ta takaita yawan 'yan kallon da za ke shiga kallon tamaula tun a shekarar 2012, a lokacin da mutane 72 suka mutu sakamakon wani yamutsi.

Haka kuma hukumar ta amince magoya baya 40,000 su kalli wasan karshe na cin kofin zakarun Afirka da za a yi tsakanin Zamalek da Mamelodi Sundowns a ranar 23 ga watan Oktoba.

A karawar farko da kungiyoyin biyu suka buga, Zamalek ce ta doke Sundowns da ci 3-0 a Afirka ta Kudu.