Madrid ta yi wasa na 400 a Gasar Zakarun Turai

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta lashe kofin zakarun Turai sai 11 sannan ta dauki Europa sau biyu
Real Madrid ta buga wasa na 400 a Gasar cin Kofin Zakarun Turai a karawar da ta ci Legia Warszawa 5-1 a Santiago Bernabéu a ranar Talata.
Wannan shi ne karon farko da kungiyoyin biyu za su kara a tsakaninsu a wasan rukuni na shida, inda Madrid ke mataki na biyu a kan teburi, ita kuwa Legia take matsayi na karshe.
Madrid ta yi wasanni 399 a Gasar ta Zakarun Turai da na Europa, inda ta ci wasanni 273 aka doke ta sau 92 ta yi canjaras a fafatawa 70, ta ci kwallaye 877 aka zura mata 427.
Real Madrid ta lashe Kofin Zakarun Turai Champions League 11 sannan ta dauki na Europa guda biyu.