Ban taba tunanin sayar da Walcott ba — Wenger

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Theo Walcott ya koma Arsenal a shekarar 2006

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce bai taba yin tunanin ya sayar da Theo Walcott a karshen kakar wasannin da aka kammala ba.

Wenger ya ce bai yi shirin ya sayar da dan kwallon tawagar Ingila ba, domin yana taka leda yadda ya kamata.

Walcoot ya yi wa Arsenal wasanni 15 a gasar Premier bara, inda ya ci kwallaye biyar, a gasar bana ya buga wa Gunners karawa takwas ya kuma ci kwallaye biyar.

Arsenal za ta kara da Ludogorets Razgrad gida da waje a Gasar cin Kofin Zakarun Turai wanda za su fara wasan farko a ranar Laraba.

Arsenal tana mataki na daya a kan teburi da maki hudu iri daya da na Paris St-Germain wadda ke matsayi na biyu.