Real Madrid ta lallasa Legia Warsaw 5-1

Champion League

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Real Madrid ta buga wasa na 400 a gasar cin kofin Zakarun Turai da na Europa

Legia Warsaw ta karbi kallaye 5-1 a hannun Real Madrid a wasa na uku a cikin rukuni na shida a Gasar cin Kofin Zakarun Turai da suka fafata a Santiago Bernabéu ranar Talata.

Real Madrid wadda ta buga wasa na 400 a gasar Zakarun Turai da na Europa, ta ci kwallayen ta hannun Gareth Bale sai Tomasz Jodlowiec ya ci gida da kuma Marco Asensio ya ci ta uku kafin a je hutu.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Madrid ta ci kwallaye biyu ta hannun Lucas Vazquez da kuma Álvaro Morata.

Legia ta ci kwallo ne ta hannun Miroslav Radovic a minti na 22 a bugun penariti.

Daya wasan na rukuni na shida Borussia Dortmund ce ta doke Sporting da ci 2-1.