Modric ya sabunta kwantiragi a Real Madrid

La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Modric ya koma Madrid da taka-leda daga Topttenham

Luka Modric ya sabunta yarjejeniyar ci gaba da buga wasa a Real Madrid zuwa kakar wasannin 2020.

Modric dan kwallon tawagar Croatia ya koma Real Madrid daga Tottenham a cikin Agustan 2012.

Ya buga wa Madrid wasanni 119 ya kuma ci kwallaye takwas, a kakar wasan bana ya yi wasanni takwas ya kuma ci kwallo daya.

Bayan da ya saka hannu kan yarjejeniya ci gaba da murza-tamaula a Madrid, kungiyar ta bashi kyautar riga mai dauke da sunansa da kuma lamba 2020.