Zan sa manyan 'yan wasa a wasan Europa — Mourinho

Europa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester United za ta buga wasanni uku a cikin kwanaki shida

Kociyan Manchester United, Jose Mourinho, ya ce zai saka manyan 'yan wasansa a karawar da zai yi da Fernerbahce a gasar Europa a ranar Alhamis.

Karawar da United za ta yi da Fernerbahce ita ce ta biyu a wasanni uku da za ta yi cikin kwanaki shida.

Manchester United ta yi canjaras da Liverpool a gasar Premier a ranar Litinin, za kuma ta buga gasar Europa a ranar Alhamis, sannan ta ziyarci Chelsea a gasar Premier a ranar Lahadi.

Sai dai Mourinho bai fadi ko zai fara wasan da kyaftin din Manchester United Wayne Rooney a karawar da za suyi da Fernerbahce a Old Trafford ba.