Uefa ba za ta hukunta Leicester City ba

Champions League

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Hukumar kwallon kafa ta Turai ta hana kunna abubuwa masu tartsatsi a ciki da wajen filin buga tamaula

Hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA, ba za ta hukunta Leicester City ba, bayan da magoya bayan FC Copenhagen suka kunna abubuwa masu tartsasi a filin King Power.

Hukumar ta kafa kwamitin bincike bisa dalilin da ya sa magoya bayan FC Copenhagen suka kunna abubuwa masu tartsatsi a karawar da ta yi a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Talata.

Uefa kan tuhumi kungiyar da ta karbi bakuncin wasan tamaula da laifi idan aka karya ka'idar hukumar a ciki da harabar fili, idan har aka sameta da sakaci.

A ranar 17 ga watan Nuwamba hukumar za ta yanke hukunci a kan kungiyar Copenhagen idan ta sameta da laifi.

Leicester City ce ta samu nasara da ci daya mai ban haushi a karawar da suka yi a Ingila.