Montreal ta sasanta da Drogba

Major League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Didier Drogba tsohon dan wasan Chelsea

Shugaban kungiyar Montreal Impact, Joey Saputo, ya ce sun sasanta kan takaddama tsakaninsu da Didier Drogba.

Kungiyar ta zargi Drogba, mai shekara 38 da kin buga mata wasa a fafatawar da ta yi da Toronto a gasar cike gurbi ta cin kofin Amurka a ranar Lahadi.

Kociyan Impact, Mauro Biello, ya ce Drogba ya ki buga wasan ne, bayan da aka gaya masa zai zauna a kan benci.

Ba a fara wasanni biyu da Drogba ba, a cikin karawa hudu da Impact ta yi a gasar ta cin kofin Amurka.

Dan wasan dan kasar Ivory Coast ya ci wa Montreal kwallaye 10 a wasanni 21 da ya yi mata a bana.