An rushe shuwagabannin Kano Pillars

Kano Pillars ta kare a mataki na bakwai a kan teburin Firimiya da aka kammala
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya rushe shuwagabannin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, saboda kasa taka rawar azo-a-gani a gasar bana.
Ganduje ya umarci shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano, Alhaji Ibrahim Galadima da ya tsara hanyar da za a nada wadanda za su maido da martabar kungiyar a fagen tamaula.
Gwamnan ya ce a lokacin da yake mataimakin gwamna ya san yadda kungiyar ta yi fice a fagen tamaula a Nigeria da Afirka, bai ga dalilin da ta gaza ba a bana.
Kano Pillars wadda ta lashe kofin Firimiyar Nigeria sau hudu, ta kare a mataki na bakwai da maki 52.
Bayan da aka kammala gasar bana ne Baba Ganaru kociyan Kano Pillars ya yi murabus daga jan ragamar kungiyar.