Barcelona ta zazzaga wa Man City kwallaye 4-0

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Barcelona ce ta daya a kan teburi da maki tara a rukuni na uku

Barcelona ta doke Manchester City da ci 4-0 a Gasar cin Kofin Zakarun Turai da suka fafata a ranar Laraba a Nou Camp.

Lionel Messi ne ya ci kwallaye uku a wasan, inda ya ci ta farko a minti na 17 da fara tamaula, bayan da aka dawo daga hutu ya kara ta biyu a minti na 61 sannan ya ci ta uku a minti na 69.

Neymar ne ya ci ta hudu saura minti daya a tashi daga wasan, kuma kafin nan ya barar da fenariti.

Manchester City ta karasa fafatawar da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa mai tsaron ragarta Claudio Andres Bravo jan kati, bayan da ya taba kwallo a wajen da'irarsa.

Ita ma Barcelona da 'yan wasa 10 ta kammala karawar, bayan da aka bai wa Jeremy Mathieu jan kati saura minti bakwai a tashi daga wasan.

Manchester City za ta karbi bakuncin Barcelona a wasa na biyu a ranar 1 ga watan Nuwamba a Ettihad.