An fitar da jadawalin gasar cin kofin Afirka

Cup of Nation

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Za a fara gasar cin kofin Afirkan daga ranar 14 ga watan Janairu zuwa 5 ga watan Fabrairun 2017

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf, ta fitar da jadawalin Gasar cin Kofin nahiyar Afirka ta 2017 a ranar Laraba.

A jadawalin da hukumar ta fitar, mai masaukin baki Gabon tana rukuni na daya da ya kunshi Burkina Faso da Kamaru da Guinea Bissau.

Rukuni na biyu ya kunshi Algeria da Tunisia da Senegal da kuma Zimbabwe, yayin da mai rike da kofin Ivory Coast da Jamhuriyar Congo da Morocco da Togo suke rukuni na uku.

Rukuni na hudu ya hada da Ghana da Mali da Masar da kuma Uganda

Za a fara gasar cin kofin Afirkan daga ranar 14 ga watan Janairu zuwa 5 ga watan Fabrairun 2017, inda za a fafata a filin Libreville da Franceville da Oyem da kuma Port Gentil da suke Gabon..