Real Madrid ta fara atisayen karawa da Bilbao

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid tana mataki na biyu a kan teburin La Liga
Real Madrid ta fara atisayen tunkarar fafatawa da Athletic de Bilbao a gasar cin kofin La Liga wasan mako na tara a ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.
A kakar bara da kungiyoyin suka kara, Bilbao ce ta sha kashi a gida a hannun Madrid da ci 2-1, yayin da Madrid ta ci wasa na biyu da ci 4-2 a Santiago Bernabeu.
Atisayen da Madrid ta yi da safiyar Alhamis ya hada da Sergio Ramos da Luka Modric da kuma Casemiro wadanda ke murmurewa daga raunin da suka yi jinya.
Haka kuma kociyan Madrid, Zinedine Zidane, ya gayyato 'yan wasan matasan kungiyar da suka hada da Enzo da kuma Odegaard cikin wadan da suka dauki horo a ranar ta Alhamis.