Onazi ya bukaci Fifa ta shiga tsakanin sa da Lazio

Lazio

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Onazi ya ce yana bin Lazio bashin albashin watan Mayu da Yuni

Ogenyi Onazi ya bukaci hukumar kwallon kafa ta duniya, ta sasanta takaddamar da ta ke tsakanin sa da Lazio, wadda ya ce yana bin kungiyar albashin watanni biyu.

Onazi dan kwallon tawagar Nigeria, mai shekara 23, ya bar Lazio da taka-leda a cikin watan Agusta, inda ya koma murza-leda da Trabzonspor ta kasar Turkiya.

Dan wasan wanda ya yi shekara biyar a Lazio, ya buga wa kungiyar wasanni 110, ya kuma ci kwallaye bakwai, ya ce ya bukaci Fifa ta shiga takaddamar bayan da kungiyar taki biyan sa hakkinsa.

Ya kara da cewar ba shi da wani zabi da ya wuce ya kai maganar gaban kwamitin ladabtarwa na Fifa domin a fitar masa da hakkinsa.

Wani jami'in Lazio wanda bai so a bayyana sunansa ba ya fadawa BBC cewar kungiyar ba za ta ce komai ba kan lamarin.