Suarez ya karbi kyautar takalmin zinare

La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Suarez ya buga wa Barcelona wasanni 12 ya ci kwallaye tara a bana

Luis Suarez ya karbi kyautar takalmin zinare a matsayin wanda ya fi cin kwallaye a kakar kwallon kafa da kasashen Turai suka yi a shekarar 2015 zuwa 2016

Suarez wanda ya karbi kyautar a ranar Alhamis, ya ci wa Barcelona kwallaye 40, a gasar cin kofin La Liga da aka kammala a Spaniya.

A gasar ta Spaniya ta bara, Cristiano Ronaldo dan kwallon Real Madrid ne ya zo na biyu da maki 35, sai Lionel Messi na Barcelona da ya ci kwallaye 26 a matsayi na uku.

A lokacin da ya karbi kyautar tare da 'ya 'yansa Benjamín and Delfina ya ce iyalansa ne suka fi mahimmaci a rayuwarsa.

Suarez ya buga wa Barcelona wasanni 12 a kakar bana, ya kuma ci kwallaye tara.