An nada sabon shugaban Kano Pillars

Nigeria

Asalin hoton, NPFL

Bayanan hoto,

Kano Pillars ta yi ta bakwai ne a gasar Firimiyar Nigeria da aka kammala

Gwamnatin jihar Kano, ta nada Muhammad Tukur Babangida a matsayin shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

Wannan ne karo na uku da Tukur Babangida zai jagoranci Kano Pillars bayan da ya yi rikon kwarya na shekara daya a 1993 da kuma karo na biyu a 2006 zuwa 2011.

Haka kuma an nada wadanda za su taimaka masa gudanar da aikin da suka hada da Musa Garba Yakasai da Faruk Sani Haladu da Tijjani Sale Minjibir da Sani Lawan da Murtala Alasan Zainawa da kuma Yahaya Idris.

Kano Pillars wadda ta dauki kofunan Firimiyar Nigeria har sau hudu, ta kammala kakar bana a mataki na bakwai a kan teburi da maki 52.