Manchester United ta ci Fernerbahce 4-1

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

United za ta ziyarci Chelsea a gasar Premier a ranar Lahadi

Fernerbahce ta sha kashi a hannun Manchester United da ci 4-1 a Gasar cin Kofin Zakarun Tutai ta Europa da suka fafata a Old Trafford a ranar Alhamis.

United ta ci kwallayen ne ta hannun Paul Pogba wanda ya ci biyu a karawar ta farko a bugun fenariti, Anthony Martial ma a bugun fenariti ya ci tasa sannan Jesse Lingard ya ci ta hudu.

Saura minti bakwai a tashi daga wasan tsohon dan wasan Arsenal da Manchester United, Robin van Persie ya farkewa Fernerbahce kwallo daya.

Da wannan sakamakon United ta hada maki shida a wasanni uku da ta buga a gasar, ita kuwa Fernerbahce tana da makinta hudu.

United za ta ziyarci Turkiya a wasa na biyu a ranar 3 ga watan Nuwamba a Gasar kofin na Europa.