Arsenal ta koma saman teburin Premier

Premier league

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Fafatawar Asernal da Middlesbrough

Kulob din Arsenal ya koma mataki na daya a teburin gasar Premier ta kasar Ingla, duk da cewa sun tashi babu wanda ya ci kwallo a fafatawar da su kayi da Middlesbrough a ranar Asabar.

Kungiyar ta Arsenal ta na da maki 20, abin da ya sa ta shiga gaban Manchester City wacce ke da maki na 19.

A ranar Lahadi ne kulob din Man City din zai kara da Southampton.

Kazalika, a fafatawar da aka yi ranar Asabar din, Burnley ta doke Everton da ci 2-1, West Ham kuma ta doke Sunderland da ci 1-0.