Dan Sama'ila ya buge Shagon Shamsi

Da
Bayanan hoto,

A turmi na biyu Dan Sama'ila ya buge Abba Shagon Shamsu

Dan Sama'ila Shagon Alabo ya buge Abba Shagon Shamsi a fafatawar da suka yi a gidan damben Ali Zuma da ke birnin Abuja na Najeriya ranar Lahadi.

Tun farko Dan Sama'ila ne daga Kudu ya wancakal da Shagon Shamsu daga Arewa a turmin farko, hakan ya sa wasan ya zo da takaddama aka ce a sake damen.

Ana kuwa sake sa zare a tsakaninsu suka dunga dukan junansu kamar ba za su bari ba, har sai da Dan Sama'ila ya kai Shagon Shamsu kasa.

Damben Shagon Mada daga Kudu da Shagon Dan Wudil Dirago daga Arewa turmi biyu suka yi, shagon Mada ya ce ba zai ci gaba ba domin Dirago ya ki tsayawa ayi amarya.

Karawa tsakanin Shagon Musan Kaduna daga Arewa da Ibrahim Kurde daga Kudu turmi daya kacal suka taka babu kisa, Tirabula ya raba su.

Shi ma wasan Garkuwan Shagon Alabo daga Kudu da na Bahagon Audu Argungu daga Arewa babu kisa.

Daga karshe aka rufe filin da gumurzu tsakanin Bahagon Sisco daga Kudu da Garkuwan Fijo daga Arewa kuma turmi biyu suka yi babu wanda yaje kasa.