Man City da Southampton sun tashi 1-1

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester City ta hada maki 20, ita kuwa Southampton tana da maki 13

Manchester City da Southampton sun tashi wasa kunnen doki 1-1 a gasar Premier da suka buga a ranar Lahadi a Ettihad.

Southampton ce ta fara cin kwallo ta hannun Nathan Redmond a minti na 27 da fara wasa, kuma da hakan aka je hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo daga hutu ne a minti na 10 Manchester City ta farke ta hannun Kelechi Iheanacho.

Manchester City za ta ziyarci West Bromwich Albion a wasan mako na 10 ranar Asabar, ita kuwa Southampton za ta karbi bakuncin Chelsea a ranar Lahadi.