Sani Kaita ya samu sabon kulob

Nigeria
Bayanan hoto,

Sani Kaita tsohon dan wasan tawagar kwallon kafa ta Nigeria

Tsohon dan wasan tawagar kwallon kafa ta Nigeria, Sani Kaita ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara daya da RoPs Rovanniemi ta Finland.

Kaita tsohon dan kwallon Kano Pillars da Enyimba ya yi atisayen makonnin biyu a kungiyar, inda daga nan ne suka cimma yarjejeniya.

Kungiyar ta RoPs ta kare gasar Finland a mataki na shida wadda aka kammala a ranar Lahadi, an kuma tafi hutu sakamakon hunturu.

Tun farko sai da Kaita ya fara yin atisaye da JS Hercules a Finland kafin RoPs ta gayyace shi filin wasanta.

Sani kaita ya buga wa tawagar kwallon kafa ta matasan Nigeria wasannin Olympic, ya kuma yi wa kasar wasannin cin kofin nahiyar Afirka da na duniya