Chelsea ta shararawa United kwallaye 4-0

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Chelsea ta ci Man United 4-0

Chelsea ta zurawa Manchester United kwallaye 4-0 a ranar Lahadi a gasar Premier wasan mako na tara da suka kara a Stamford Bridge.

Chelsea ta ci kwallayen ne ta hannun Pedro Rodriguez kasa da minti daya da fara wasa, sannan Gary Cahill ya ci ta biyu saura minti 24 a je hutu.

Bayan da aka dawo ne da hutu Chelsea ta kara kwallo na uku ta hannun Eden Hazard, sannan N'Golo Kante ya ci ta hudu saura minti 10 a tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon Chelsea ta hada maki 19 ta kuma koma mataki na hudu a kan teburin Premier, yayin da United ta ci gaba da zama a matakinta na bakwai da makinta 14.

United wadda ta kara da Liverpool da Fernerbahce da Chelsea a cikin kwanaki shida, za ta karbi bakuncin Burnley a ranar Asabar.

Ita kuwa Chelsea za ta ziyarci Southampton a wasan mako na 10 a ranar Lahadi a gasar ta Premier.