Real Madrid ta dare kan teburin La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta koma mataki na daya a kan teburi
Real Madrid ta samu nasara a kan Athletic Bilbao da ci 2-1 a gasar La Liga wasan mako na tara da suka fafata a ranar Lahadi.
Karim Benzema ne ya fara ci wa Madrid kwallo a minti na bakwai da fara tamaula, kuma a minti na 28 Bilbao ta farke ta hannun Sabin Merino.
Saura minti takwas a tashi daga wasan Alvaro Morata ya ci kwallo na biyu, wanda hakan ya bai wa Madrid damar samun maki uku a fafatawar.
Da wannan sakamakon Real Madrid ta dare mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 21, Sevilla ce ta biyu da maki 20, sai Barcelona mai maki 19 a matsayi na uku.