Sanches ya lashe kyautar matashin dan kwallon Turai

Europe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Renato ya yi wa Bayern Munich wasanni takwas a kakar bana

Dan wasan Bayern Munich, Renato Sanches, ya lashe kyautar matashin dan kwallon kafa da ya fi yin fice a nahiyar Turai.

Hakan ne ya sa Sanches ya doke abokin takararsa matashin dan kwallon Manchester United, Marcus Rashford.

Sanches ya bi sahun Wayne Rooney da Raheem Sterling da Lionel Messi da kuma Sergio Aguero a matsayin wadan da suka lashe kyautar suna da kasa da shekara 21.

Dan wasan ya buga wa Bayern wasanni takwas a kakar bana, ya kuma yi wa tawagar kwallon kafa ta Portugal wasanni 11.

A gasar da aka yi a Faransa ta cin kofin nahiyar Turai Sanchez wanda a lokacin yana da shekara 18, shi ne ya lashe kyautar matashin dan kwallon da ya fi yin fice a gasar.

Jaridar Tuttosport ta Italiya ce ta kirkiro kyautar a shekara 2003, wadda ta bayyana gwarzon bana a farkon shafinta da ta wallafa.