FA ta tuhumi Sissoko da laifin yi wa Arter gula

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Moussa Sissoko dan kwallon tawagar Faransa

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi dan wasan Totteham Moussa Sissoko, da laifin yi wa Harry Arter na Bournemouth gula.

Sissoko ya aikata laifin ne a lokacin da kungiyoyin suka tashi wasa babu ci a gasar Premier na mako na tara a ranar Asabar.

Hukumar ta ce alkalin wasa bai ga laifin ba, amma za ta bayar da faifan bidiyon wasan ga wani kwamitin mutane uku da ta nada domin yanke hukunci.

An bai wa Sissco nan da ranar Talata domin ya kare kansa, idan ba haka ba za a iya dakatar da shi daga buga wasannin Premier uku.

A makon jiya an dakatar da Sergio Aguero na Manchester City, bayan da aka same shi da laifin yi wa Winston Reid na West Ham gula.