Liverpool za ta karbi bakuncin Tottenham a League Cup

League Cup

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Liverpool da Tottenham sun buga 1-1 a gasar Premier ta bana da suka kara a White Hart Lane

Tottenham za ta ziyarci Anfield domin karawa da Liverpool a gasar League Cup wasannin zagaye na hudu a ranar Talata.

Kungiyoyin biyu sun kara a gasar Premier ta bana a cikin watan Agusta a White Hart Lane, inda suka tashi wasa kunnen doki 1-1.

Sauran wasannin da za a buga a ranar ta Talata, Arsenal za ta karbi bakuncin Reading, Preston kuwa Newcastle United za ta ziyarta.

Leeds United kuwa za ta karbi bakuncin Norwich City ne.

Ga wasannin da za a buga a ranar Laraba:

  • Southampton vs Sunderland
  • West Ham vs Chelsea
  • Man Utd vs Man City