U-20: An fitar da jadawalin gasar matasa ta Afirka

CAF
Bayanan hoto,

Za a yi wasannin matasan ne a Zambia a shekarar 2017

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf, ta fitar da jadawalin gasar cin kofin matasa 'yan kasa da shekara 20 da za a yi a kasar Zambia.

Hukumar ta fitar da jadawalin ne a Masar a ranar Litinin.

Rukunin farko ya kunshi Zambia mai masaukin baki da Guinea da Masar da Mali.

Rukuni na biya ya hada da Senegal da Sudan da Kamaru da Afirka ta Kudu.

Za a fara buga gasar a ranar 26 ga watan Fabrairu zuwa 12 ga watan Maris din 2017 a Zambia.

Duk wadanda suka kai wasan daf da karshe ne a gasar za su wakilci Afirka a wasannin cin kofin duniya ta matasan da za a yi Korea a shekarar 2018.