Audu Mai Kaba ya koma kocin Akwa United

Nigeria Premier League
Bayanan hoto,

Audu Mai Kaba ya kai Wikki Tourist matsayi na uku a gasar Firimiyar Nigeria da aka kammala

Audu Mai Kaba ya cimma yarjejeniyar horar da kungiyar kwallon kafa ta Akwa United zuwa Shekaru biyu.

Mai Kaba wanda ya ja ragamar Wikki Tourist zuwa mataki na uku a kan teburin Firimiyar Nigeria da aka kammala, bai saka hannu a kan kwantiragin ba tukunna.

Kociyan wanda ya yi mataimakin kociya a kungiyoyin da suke buga Firimiya sau da dama, ya horar da Kano Pillars da Enyimba International.

Akwa United ta garin Uyo ta kare a mataki na 14 a kan teburin Firimiyar kasar da aka kammala da maki 47.

Mai Kaba yana cikin masu horarwa da suka ja ragamar tawagar kwallon kafa ta Super Eagles masu taka leda a Afirka da suka yi wasanni a Spaniya.