Man United za ta karbi bakuncin Man City a League Cup

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

City ce ta doke United 2-1 a wasan farko da suka kara a gasar Premier

Manchester City za ta ziyarci Old Trafford domin karawa da Manchester United a gasar League Cup wasannin zagaye na hudu a ranar Laraba.

A cikin watan Satumba kungiyoyin biyu sun kara a gasar Premier a Old Trafford, inda City ta ci United 2-1.

United wadda ta sha kashi a hannun Chelsea 4-0 a gasar Premier a ranal Lahadi, za ta yi wasa na Hudu a cikin kwanaki tara, bayan da ta tashi babu ci da Liverpool a ranar Litinin.

Kungiyar ta doke Fernerbahce a gasar cin kofin Zakarun Turai na Europa a ranar Alhamis, sannan Chelsea ta casa ta a gasar Premier a ranar Lahadi.

Wasa na biyu da za a buga a ranar Laraba kuwa, West Ham United za ta karbi bakuncin Chelsea a gasar ta League Cup.

A cikin watan Agusta ne a kakar wasan bana Chelsea ta ci West Ham 2-1 a gasar Premier da suka fafata a Stamford Bridge.