De Bruyne ba zai buga karawa da Man United ba

League Cup

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

De Bruyne yana jinya, ba zai buga wasan hamayya a Old Trafford ba

Dan wasan Manchester City, Kevin de Bruyne, ba zai buga karawar da kungiyar za ta fafata da Manchester United a gasar League Cup ba, sakamakon rauni da yake jinya.

Shi ma Pablo Zableta ba zai samu damar buga wasan ba, saboda raunin da ya yi, amma kyaftin din kungiyar Vincent Kompany ya murmure zai kuma yi wasan na hamayya.

Kociyan City, Pep Guardiola, wanda kungiyarsa ta kasa cin wasanni biyar a jere, ya ce zai sauya wasu 'yan wasan da suke buga wa kungiyar kwallo a kullum.

Ita ma United ba ta ci wasan Premier ba a cikin watan Oktoba, kuma a ranar Lahadi Chelsea ta casa ta da ci 4-0 a Stamford Bridge.