Eric Bailly zai yi jinyar wata biyu

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bailly ya koma Manchester United da taka a cikin watan Yuni

Mai tsaron baya na Manchester United, Eric Bailly, na fatan ya warke daga raunin da ya yi a gwiwar kafarsa nan da watanni biyu masu zuwa.

Bailly dan kwallon tawagar Ivory Coast, mai shekara 22, ya yi rauni ne a lokacin da ya yi karo da Eden Hazard a gasar Premier da Chelsea ta casa United 4-0 a ranar Asabar.

Bayan kammala karawar kociyan Manchester United, Jose Mourinho, ya ce ya tsorata da raunin da dan kwallon ya yi, kar ya kai shi doguwar jinya.

Bailly ya yi wa United dukkan fafatawar da ta yi a wasannin kakar bana, ya kuma koma Old Trafford da taka-leda daga Villarreal kan kudi fam miliyan 30 a bana.