Liverpool ta fitar da Tottenham daga League Cup

League Cup

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sturridge ya ci kwallaye tara a wasanni takwas da ya buga a gasar League Cup

Liverpool ta kai wasan zagayen gaba a gasar League Cup, bayan da ta ci Tottenham 2-1 a karawar da suka yi a ranar Talata.

Liverpool ta ci kwallon farko ta hannun Daniel Sturridge a minti na tara da fara wasa, bayan da aka dawo ne ya kara cin ta biyu.

Tottenham ta farke kwallo daya ne a bugun fenariti ta hannun Vincent Janssen saura minti 12 a tashi daga fafatawar.

Ita ma Arsenal ta kai wasan zagayen gaba bayan da ta ci Reading 2-1, Newcastle United kuwa shararawa Preston North End kwallaye 6-0 ta yi.

Ga sakamakon wasannin da aka yi:

  • Arsenal 2 : 0 Reading
  • Liverpool 2 : 1 Tottenham Hotspur
  • Bristol City 1 : 2 Hull City
  • Leeds United 1 : 1 Norwich City
  • Newcastle United 6 : 0 Preston North End