Har yanzu Guardiola na jiran Toure ya nemi gafara

getty

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Guardiola ne ya sayar da Toure ga Manchester City daga Barcelona a shekarar 2010

Har yanzu kociyan Manchester City, Pep Guardiola, na jiran mai kula da harkokin kwallon kafar Yaya Toure ya ba shi hakuri.

Dimitri Seluk ya ce kociyan ya ci mutuncin dan wasan, bayan da ya bukaci sai an ba shi hakuri kafin ya ci gaba da sanya shi a wasanni.

Wasa daya Toure kyaftin din Ivory Coast ya buga wa City a lokacin da ta fafatawar a wasannin cike gurbin shiga Gasar Kofin Zakarun Turai.

A cikin watan Satumba Guardiola ya nemi da Seluk ya bashi hakuri idan yana son Toure ya ci gaba da buga wa City kwallo.

Shi kuwa mai kula da wasan dan kwallon ya shaida wa BBC cewar "don me zai bayar da hakuri; ya kamata ya tattauna da Toure wanda shi ne ke taka-leda.

Har yanzu babu wanda ya nemi afuwar tsakanin Seluk ko kuma Toure a wurin kociyan.