An ci tarar Valencia saboda jefa robar ruwa cikin fili

La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Barcelona ce ta lashe karawar da ci 3-2 a wasan mako na tara da suka yi ranar Asabar

Hukumar kwallon kafa ta Spaniya ta ci tatar Valencia kudi fam 1,340 bayan da magoya bayanta suka jefi 'yan wasan Barcelona a gasar La Liga ranar Asabar.

Hukumar ta kuma ja kunnen kungiyar cewar idan hakan ya sake faruwa za ta rufe filinta na Mestalla.

Kungiyoyin biyu sun kara ne a wasan mako na tara na gasar La Liga ranar Asabar, inda Barcelona ta lashe karawar da ci 3-2.

Magoya bayan Valencia sun yi ta jefa robar ruwa a kan 'yan wasan Barcelona a lokacin da suke murnar cin kwallo na uku da Messi ya ci a bugun fenariti.

Luis Suarez da Neymar sun fadi kasa a cikin filin lokacin da robobin ruwan suka sauka a kan 'yan wasan.